Wednesday 27 February 2019

Dr Ahmed Qalam, ya kai ziyara ga kungiyar Hausawan Sudan ta kasa da kasa a kasar belgium




Ranar: 15 Fabrairu 2019
 Shugaban kungiyar Hausawan Sudan ta kasa da kasa ofishin belguim Naziru Ibrahim da Idrisu Mohamed Ibrahim sun karbe shi  daga babban filin Jirgin Kasar belguim wato na Brussel, wanda ya zo daga Kasar Rasha wurin zamanshi. ziyara ta kwana uku,
A lokacin da ya gana da membobin kungiya a ofishin ta na Belgium, sun tattauna a kan nasarorin da kungiya ta yi a shekarun da suka gabata , kuma da aiyukan da take su ta yi an gaba, daga bisane sun bashe damar  tofa albarkaci bakinsa, sai ya fara da godiya da nuna farin cikin sa a kan kyakyawar taryar da aka masa, daga nan sai ya nuna aiyukan da kungiyar sa ta ke yi suna kama da na Kungiyar mu daga nan sai ya sake nuna farin cikin sa da jinjinawa yan Kungiya a kan namijin  kokarin da suke na aikin  taimako kuma ya bada goyan baya sa ga wannan kungiya dare bias dare kuma ya ce daga yau ya zama yana daya daga cikin mimbobin wannan Kungiya kuma ya mana albishiren bada gudun mawar sa ta kowace hanja don ya tabbatar Kungiyar mu ta tsaya da kafofin ta. dokta Ahamed she dai likita ne dan sudan yana zaune a kasar Rasha kuma she mutun ne mai gwazo da basira kuma she kwararre ne a aikin tiyata. kuma yanada kishe Hausa sosai, she yasa ya takanas ya zo don yagana da yan kungiyar hausawa.
Daga garshe muna mika godiyar mu  da jinjina masa da tattakewar da yayi yazo mana.

Gaisuwa ta musamman
Dag magatakardar kungiya




No comments:

Post a Comment