Sunday, 26 August 2018

Ranar hausa ta duniya


Ma'abota shafukan sada zumunta na zamani na bikin ranar Hausa ranar Lahadi.
Wani mai fafutika a shafukan zumunta kuma mai sha'awar inganta harshen Hausa, Abdulbaqi Jari da wasu abokansa ne suka kirkiro ta domin raya harshen Hausa da kuma inganta amfani da shi a kan shafukan sada zumunta. Ana gudanar da bikin #RanarHausa a kowacce ranar 26 ga watan Agusta.
An fara bikin ne a shekarar 2015, inda a wannan shekara ta 2018, ake yin sa karo na hudu

No comments:

Post a Comment