Sunday 26 May 2019

Taron Buda bake na Kungiyar Hausawan sudan ta kasa da kasa ofishin Gadare


ƙungiyar hausawan Sudan ta ƙasa da ƙasa
Reshen sudan ofishin jahar (gadare )
ranar 8 ga watan azimi wanda yai daidai da 13/05/2019 Ofishin Gadare yayi taron buɗa baki a karamar hukumar gadare.
Wannan taro ysamu halatar mutane sama da mutun ɗari, aikin su hada wasu manya manyan Hausawan Jihar masu faɗa aji a wasu ƙabilun da suke zaune tare da Hausawa.
bayan buɗa baki nan take sai wani ya tashe yagabatar da mutane uku domin faɗakarwa a taƙaice saboda ƙarancin lokaci tsakanin sallar magariba da isha,i.
da farko angabatar Mallam izaddin abakar wanda shi malami ne babba afannin ilimin addini wanda ya kawo bayanai a taƙaice akan matasa da kuma ƙungiyoyi masu temako akan abun buɗa baki ga masu azimi da falalar yin hakan
daga bisani ya yaba aikukan da kungiyar hausawa ta ƙasa da ƙasa ta keyi na takmaka masu galiho da kuma ƙoƙarin da take na taimakawa marayo da masu ƙaramin ƙarfi a kan su ji gaba da karato malamin ya yi tsokaci ga iyayan yara a kan lura da tarbiyar su da kula da lafiyar su domin sune manyan gobe
mutun na biyu ~wanda shine mai kula da aiyukan ƙunƙiyar a jahar gadare wato ɗan uwanmu (atayif ahmad)wanda shima ya kawo bayanansa a taƙaice wanda yayi bayanin sa akan wayar wa da jama, a kan muhimmancin shiga ƙungiya da kuma bada gudun mawar su akan kaikin taimakon Al’uma da hadin kai kuma yai bayani akan muhimmancin karato ga yara mata da maza y ace domin muhimmancin sa manzon Allah y ace a nimi Ilimi ton ranar haifuwa har ranar ƙareshe, kuma ya ƙara da cewa awnnan ƙungiyar ta kawo cigaba sosai musammam ta ɓangaren sauya makarantun allo na gargajiya zuwa makarantun zamani, aikin da take a yanzunnan ya ishemu shaida wanda ta ginia aje na farko a makarantar Abdallah bin masoud ta garagjiya a jahar farin koji birnin rabak
daga garshe sai ya mikawa wani malamin makaranta domin ya cigaba da wayarwa bias ilimi da tarbiyar yara .
wato shine mutun na uku mallan anas ali wanga she shugaban wata makaranta ne a gadare sannan yayi karatun kimiyya a tarbiya wanda yai bayani mai ratsa jiki inda yace wannan lokaci ne na ilimi wanda bayada ilimi ya zame abin ware domin yanzu kowaci irin haraka za kayi said a ilimi shiyasa yace ya kamata mu fito matan da mazan mu ƙwatowa kan mu ince a neman ilimi yanda manzun Allah y ace niman ilimi farilla ce ga duka musulmi maza da mata
kuma y ace duka matsalolin da Hausawa suke samu yana dangana a kan rashin ilimi kuma da auren uwri , daga nan sai ya miƙa saƙonsa ga matasa mata da maza a kan jajircewa su ga sun kamala karatun su har samun manyan maƙamai yawa dr da frofisa sa sauransu daga ƙarshe sai ya tabo matasan da busuyi karatu ba y ace suyi ƙoƙari su sanu sana’a domin samu kyakyawar rayuwa
daga ƙarshe ya miƙa godiyar sag a wannan ƙungiya mai manufofi ma su kyau yana cewa yana fatan Allah ya ƙara ƙarfafa gwiwar masu tafiyar dawannan ƙungiyar














No comments:

Post a Comment