Da sunan Allah mai
rahama mai jikai
kungiyar hausawan
Sudan ta ƙasa da ƙasa
reshen sudan ofishin
jahar( sinnar) karamar hukumar (amshoka)
ranar 19 ga watan azimi wanda yayi daidai da
ranar 24/05/2019 tayi gaga rimin
taron buɗa baki a jahar ta sinnar wanda ya sami halar tar mutane da dama sosai
daga ƴan garin bayan anyi buɗa bakin sai aka soma tattaunawa inda ɗan uwan mu
wato ( umar abubakar ) wanda shi ma aikacine a ma'aikatar labarai ta ofishin
jahar sai malan (abdul'aziz abdullah)wanda yana cikin wanda suka tsaya sosai
wajen ganin an ƙaddamar da makarantar alya'fien ) sannan sai maganar malan
(hamza yusuf ) wanda shine yazo amatsayin wakilin (dindir) sai mai wakiltar
(faƙad ) wato ali muhammad ) sannan sai maganar mai wakiltar kungiyar (amshoka)
malan anas mustafa) yakasance anrife taron da maganar shugaban ofishoshi na
jahar wato malan (babikir ali umar ) wanda ya soma da godewa wanda su suka soma
wannan farar tafiya mai farin aiki da zummar allah ya saka musu da alkairi amen
kamar irin su dakta ( hasan waƙi allah) da ( dakta ahamed ali ) muna tawasali
da wannan aiki da sukai allah yasa saka musu da mafificin alkairi amen sannan
yai bayani akan wannan ƙungiya akan aiyukan ta da takeyi musammam yadda tame da
hankali akan karantar wa da tarbiyantar da yara wanda sune manyan gobe sannan
ya fadakar akan matasan wannan ƙabila da su kula sannan su guji duk wani tashin
hankali da zai shafemu da kuma ƙabilar mu baki ɗaya sannan ya tsananta akan
kungiya da aikinta da ta kula da duk wata ɓaraka da ta tasowa wannan ƙabila
baki ɗaya sai magana ta shida wacce shugaban kungiyar na amshoka yayi bayan
haka sai taron ya ƙare wanda hakan ya ƙara sa jituwa tsakanin matasan )
amshoka) da na dindir) da na faƙad) da na murafa) kamar yadda kungiyar ta ke
miƙa godiyar ta ga wayenda suka temaka da lokacinsu da karfinsu da kuɗinsu
sanarwa daga ofishin jahar
No comments:
Post a Comment